Sũratun Najm.Tanã tsarkake Annabi da Manzancinsa daga kõwane aibi. Tanã tabbatar da Shi daga Allah, sa’an nan tanã ɓãta dukan abin da bã shi ba na addĩnai da al’ãdu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. 1. Inã rantsuwa da taurãron, a
lõkacin da ya faku.
2. Ma'abũcinku bai ɓata ba,
kuma bai ƙħtare haddi ba.
3. Kuma bã ya yin magana daga
son zuciyarsa.
4. (Maganarsa) ba ta zamo ba,
fãce wahayi ne da ake aikõwa.
5. (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi
(1) ya sanar da shi.
6. Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini,
sa'an nan ya daidaita.
7. Alhãli kuwa yanã a sararin
samã mafi aukaka.
8. Sa'an nan ya kusanta, kuma
ya matsa zurõwa.
9. Har ya kasance gwargwadon
zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi
kusa.
10. Sa'an nan ya yi wahayi zuwa
ga bãwan Allah (Muhammadu) da
abin da ya faɗa (masa ).
11. Zũciyar (Annabi) bata
ƙaryata abin da ya gani ba.
12. Shin, zã ku yi masa musu a
kan abin da yake gani?
13. Kuma lalle ya gan shi,
haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa
(2) .
14. A wurin da magaryar tuƙħwa take.
15. A inda taken, nan Aljannar
makoma take.
16. Lõkacin da abin da yake rufe
magaryar tuƙħwa ya rufe ta.
17. Ganinsa
(3) bai karkata ba,
kuma bai ƙetare haddi ba.
18. Lalle, tabbas, (Annabinku)
ya ga waɗanda suka fi girma
(4) daga ãyõyin Ubangijinsa.
19. Shin, kun ga Lãta da
uzza?
(5)
20. Da (wani gunki wai shi)
Manãta, na ukunsu?
21. Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ
(Allah) kuma da ɗiya mace?
22. Wannan fa ya zama rabo
naƙasasshe.
23. Waɗannan bã kõme ba ne
fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace
su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai
saukar da wani dalĩli game da su ba.
(Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato
da abin da rãyukansu ke so, Alhãli
kuwa shiriyar
(6) ta daga wajen
Ubangijinsu, ta jħ musu (sai suka
bar ta suka kõma wa zaton).
24. Ko (an fai cħwa) mutum zai
sãmi abin da yake gũri?
25. To, Lãhira da dũniya na
Allah kawai ne (wanda ya nħme su
daga wani, yã yi kuskure).
26. Akwai malã'iku da yawa a
cikin sammai cħtonsu bã ya
wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi
izni (da shi) ga wanda Yake so,
kuma Yake yarda.
(1) Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu
mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabiya san shi sõsai,
kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan
shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa.
(2) Lamirin Malã'ika Jibrila ne.
(3) Lamirin Malã'ika Jibrila ne.
(4) Watau dai Alƙur'ani ya zo daga Allah ta hanya mafi aminci har ya sadu da
mutãne dõmin su yi aiki da abin da ke cikinsa.
(5) Watau kun bar Alƙur'ani kun kõma wa surkullen da kuke haɗãwa game da
gumãka su Lãta da Uzza da Manãta. Kuna cħwa sũ wakĩlan Mala'ikun da kuke bautã wa ne kuma su 'ya'yan Allah mãtã ne. Sunã cħton ku daga Allah.
(6) Watau Alƙur'ani wanda Mala'ika jibrĩla ya zo wa Annabi da shi. Sun bar shi sun kõma wa tatsũniyõyi da gũrace-gũrace.