Sũratul Isrã’.Tanã karantar da daidaitãwa a tsãkãnin abũbuwa mãSu dangantaka da jũnã.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. 1. Tsarki ya tabbata ga wanda
Ya yi tafiyar dare
(1) da bãwanSa da
dare daga Masallaci mai alfarma
zuwa ga Masallaci mafi nĩsa
(2)
wanda Muka sanya albarka
a gefensa dõmin Mu nũna masa daga
ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai
ji, Mai gani.
2. Kuma Mun bai wa Mũsã
(3)
littafi, kuma Mun sanya shi shiriya
ga Banĩ Isrã'ila, cħwa kada ku riƙi
wani wakĩli baiciNa.
3. Zuriyar waɗanda Muka ɗauka
tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya
kasance wani bãwa mai gõdiya.
4. Kuma Mun hukunta zuwa ga
Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa
lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa
sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci,
zãlunci mai girma.
5. To idan wa'adin na farkonsu
yajħ, za Mu aika, a kanku waɗansu
bãyi
(4) Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ
tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin
gidãjenku, kuma yã zama wa'adi
abin aikatawa.
6. Sa'an nan kuma Mu
mayar da
ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu
taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya
kuma Mu sanya ku mafiya yawan
mãsu fita yãƙi.
7. Idan kun kyautata, kun
kyautata dõmin kanku, kuma idan kun
mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan
idan wa'adin na ƙarshe
(5) ya jħ,
(za su je) dõmin su baƙanta
fuskokinku, kuma su shiga
masallaci kamar yadda suka
shige shi a farkon
lõkaci, kuma dõmin su halakar da
abin da suka rinjaya
a kansa, halakarwa.
(1) Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli.
(2) Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji
a Ɗũr-Sĩna'a.
(3) Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba.
(4) Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu.
(5) Suka yi fasãdi marra ta biyu da kashe
Zakariyya da Yahaya,
sai aka aika musu da Bukht Nasar daga Bãbila ya karkashe su, kuma ya kãma zuriyarsu, kuma ya rũshe Baitil
Maƙadis. Waɗannan lãbaru biyu na ɓarnar Banĩ Isrã'ila sunã cikin bãyar da lãbaru ga gaibi. Idan an daidaita su da lãbarun gaibi waɗanda Alƙur'ãni ya faɗã, waɗansu suka auku
kuma waɗansu sunã ta aukuwa zã a san falalar Alƙur'ãni a kan Taurãti kamar yadda ya bayyana cħwa Attaura ta yi kira zuwa ga tauhidi da shiriya, sa'an nan ya bayyana abũbuwan da Alƙur'ãnĩ yake karantarwa daga ãyã ta 9 zuwa ga ãyã ta 38 inda ya tãra
hãlãyen ƙwarai kuma ya kõre mũnãna.