الترجمات
   
إذاعة القرآن الكريم دليل الموقع تنزيل مواد مجانا
لوحة المفاتيح العربية في الموقع في القرآن بحث بحث متقدم
الصفحة:
 الجزء:   السورة:
  رقمها:
  الآية:

Hausa Translation: Page 1

Sũratul Fãtiḥa.
Ãyõyinta 7 ne. Anã kiranta Uwar Littafi dõmin tã tãra ilmin da yake a cikin Alƙu’ãni a dunkule. Bãsmala a cikinta take ga ƙirã’ar Ãsim, ruwãyar Hafs, ammã banda ga kirã’ar Warsh.

  1. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

  2. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;

  3. Mai rahama, Mai jin ƙai;

  4. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.

  5. Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.

  6. Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.

  7. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.(1)

   (1) Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilmin tauhidi na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar dũniya mai dõgħwa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma Kai muke nħman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce-hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi, yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu, yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata.
 
  صفحة  1 \ 604  تالي 

الأسئلة المتكررة  ..  أخبر صديقا  ..  اتصل بنا  ..  سجل الزوار
تحميل برامج مجانية

   
      القــرآن الكــريم
      عـلــوم القــرآن
      تفاســير القــرآن
      الــترجمـــــات
      فتاوى تتعـلق بالقـرآن
      تاريخ المصحف الشريف
      فهرست مصنفات التفسير
      آيـــة وحــديـث
      نماذج من الخط العربي
      تحميل خطوط المصحف
      مواقع المجمع
      برامج الندوات
      مـــن نــحــن؟



أعلى الصفحة
جميع الحقوق محفوظة لمجمع الملك فهد لطباعة المصحف الشريف