Sũratul Fãtiḥa.Ãyõyinta 7 ne. Anã kiranta Uwar Littafi dõmin tã tãra ilmin da yake a cikin Alƙu’ãni a dunkule. Bãsmala a cikinta take ga ƙirã’ar Ãsim, ruwãyar Hafs, ammã banda ga kirã’ar Warsh.
1. Da sũnan Allah, Mai rahama,
Mai jin ƙai.
2. Godiya ta tabbata ga Allah,
Ubangijin halittu;
3. Mai rahama, Mai jin ƙai;
4. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
5. Kai muke bauta wa, kuma
Kai muke neman taimakonKa.
6. Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
7. Hanyar waɗanda Ka yi wa
ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi
ba, kuma ba ɓatattu ba.
(1)
(1) Da cewa Ubangijin halittu ya tara
ilmin tauhidi
na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama
Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da
ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar
dũniya mai dõgħwa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma
Kai muke nħman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce-hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi,
yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu,
yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata.